Kamfanin dillancin labaran Ahl al-Bait (AS) - ABNA - ya habarta cewa, kimanin watanni bakwai bayan sakin Sheikh Muhammad Al-Abad, fitaccen malamin Shi'a, gwamnatin Saudiyya ta sake kama shi ba tare da wani dalili ko hujja ba.
An kama Sheikh Muhammad Al-Abad daga garin Al-Omran a lardin Al-Ahsa a ranar 16 ga Satumba, 2019 kuma aka kai shi wani wuri da ba a sani ba. A wancan lokacin ne kotun Saudiyya ta yanke wa Sheikh Al-Abad hukuncin daurin shekaru biyu da rabi tare da haramta masa yin balaguro na tsawon lokaci guda.
A cewar Miraat Al Jazeera, ya kasance a gidan yari na kimanin shekaru 3 kafin a sake shi a watan Maris 2022. An kama Sheikh Al-Abad ne saboda Tsayin dakarsa da jajircewarsa wajen kare hakkin 'yan kasa da sukar cin hanci da rashawa da kuma ayyukan Al Saud suke aikatawa.