Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

3 Oktoba 2022

20:04:23
1310260

Bayanin Sayyid Hasan Khumaini Biyo Bayan Jawabin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci 03/10/2022

Bayanin Sayyid Hasan Khumaini Biyo Bayan Jawabin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci 03/10/2022

Bayan Jawabin Da Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Yi A Yau Dangane Da Abubuwan Da Suka Faru A Kasar, Yadgar Imam Ya Fitar Da Bayani.

Nassin Bayanin Hujjatul Islam Wal Muslimin Na Sayyid Hasan Khumaini Shi Ne Kamar Haka;


Ina so in yi magana game da "abubuwan da suka faru a kwanakin nan" kafin yin wannan bayanin na jagora, amma saboda tashe-tashen hankula a cikin al'umma gaba ɗaya, na bar shi zuwa lokacin da ya dace. Amma a yau yayin da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya nemi cewa kowa ya iya fitar da ra’ayinsa akan abun yak e faruwa na baya bayan nan. Sai yazo mun aria na rubuta wasu yan jumloli dangane da hakan: 

1-Ko shakka babu akwai bambanci tsakanin “Zanga zangar lumana” wacce ita hakki na shari’a ga kowane dan kasa, da kuma “hargitsi” wanda ya samo asali daga makircin makiyan al’umma. Zanga-zangar alama ce ta rayuwar al'ummar da ba ta da wata barna, amma hargitsi da karya ka'idoji - wanda kuma kafafen yada labarai suka rura wutar ba tare da tausaya wa al'ummar Iran ba – wanda yake sakamakon hakan bai ya wuce mulkin wuce gona da iri da hargitsi ba. Kar mu manta cewa kafafen yada labarai da suka haifar da baraka a tsakaninmu a yau ko dai sun yi kiyayya da mu, ko kuma sun mayar da rayuwarsu daga wani waje da a kullum ake kiran Iran da Iraniyawa masu rauni.

Ba mu da wani zabi face mu zauna muyi rayuwa da juna gaba dayanmu da Dukkanmu kasa daya ce mai yanayi da dandano da hasashe iri daya; Tare da fahimta daban-daban amma da take dauke da manufa ɗaya. Abin alfaharin kasarmu yana samuwa ne ta hanyar zaman lafiya tare da tsayawa tsayin daka agaban masu son wulakanta mu. Dole ne mu tattauna da juna; Bangarorin jama’a tare da gwamnati su zauna tare da masu tunanin sabanin haka. Kuma ba shakka, kada mu yi tantama cewa yaƙi da addini da yaƙi da abin da ake kira “Kimar addini” a idon jama’a ba zai yiwu ba kamar yaƙi da ‘yanci da wadata.


2-Tattaunawa ita ce hanya daya tilo da za ta fitar daga cikin rudani. A bayyane yake cewa ba mu fuskanci zanga-zangar bangare daya ba. Kuma a wasu lokutan zayyiwu a fuskanci zanga zanga daga ƙarama ko babbar ƙungiya mai fahimta daban-daban na iya adawa da wata manufa ko ɗabi'a. A cikin wannan al'umma, masu zanga-zangar da hukumomin gwamnati ba su da wani zabi illa su shiga tattaunawa tare da dukkanin sharuddan da suke da su, wanda shi ne mafi dacewa don gyarawa.

Idan kuma a daya bangaren, manyan take-take da hayaniya ba su yi tasiri ba, to kuma dole ne tsarin siyasa ya fara tattaunawa da bangarori daban-daban na al’umma, a kuma saurari radadin da suke ciki, idan ya cancanta a ba su uzuri-wanda ya kasance abun ya dau lokaci mai tasyi yana ma hakin dushewa sannu a hankali. 

A dabi'ance ne cewa sakamakon wannan tattaunawa ba zai kasance ci gaba da "rashin sassauci a wasu hanyoyi da dabi'u ba", kuma ba zai dace da buƙatun rushewa ba. Kuma daga waɗannan zance ne ake samun gwargwado na sassauci da ma'anar rushewa.


3- A yau, raɗaɗi iri-iri sun yi nauyi a kan rayuwar mutane, abin da ya fi muhimmanci shi ne batun rayuwa da matsalolin tattalin arziki. Magance duk wata matsala a wasu bangarori na bukatar gyara a harkokin tattalin arziki. Ya kamata gwamnatin jarumana mazaje ta sani cewa idan ba za su iya magance matsalolin tattalin arziki ba, a kodayaushe zai zamo suna bada hanyar haifar da tarzoma da cin zarafi daga wajen baki.


4- Wani babban bangare na zanga-zangar da bacin rai na mutane yana faruwa ne saboda rufe hanyoyin shari'a na zanga-zangar wanda ya zamo akwai bukatar canza wasu dokoki da manufofin shari'a da na siyasa da suka dace. Ko shakka babu bude hanyar halartar kowane irin fahimta a cikin ginshikan gwamnati zai toshe hanyoyin makiya. Don rage karfin kasancewar Amurka da gwamnatin masu cin zarafi da kawayenta, dole ne mu samar da karfin tsarin a cikin sa hannun dukkan bukatu a cikin doka da aiwatarwa.


5- Matsayin Jagoran juyin juya halin Musulunci, wanda baya ga matsayinsa na shari'a, ya kebantu da kyawawan halaye, kuma yana daga cikin jagororin zamaninsa, yana da daraja ta musamman ga duk wani wanda ya san shi daga nesa ko kuma makusanci, kuma ga mafi yawan al'umma daga Suna da irin wannan girmamawa ta yadda cin zarafin su babban cikas ne ga kowace irin fahimta da tattaunawa. Bugu da kari, a bayyane yake ga duk wanda ya san siyasa cewa lafiyarsu na da alaka mai zurfi da zaman lafiyar kasa da kuma al'amura.


6- Jamhuriyar Musulunci ta kasance sakamakon tsarkakakken jinin da aka zubar a doron kasa don neman yardar Allah da kuma bin Imam mai girma da fatan jin dadin mutane. Wajibi ne ga duk wanda ya dauki kansa da wannan lamari na musamman, su kiyaye ta, da kuma gyara ta da watsi da kurakuransa, tare da kare hakikaninta.


Daga karshe ina rokon Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu a cikin abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, wadanda suka jikkata kuma ya basu lafiya, da kuma walwala ga jami’an tsaro, da nasara, ga kuma dukkan al’umma da su samu sauki cikin ranakun farin ciki daga Allah Madaukakin Sarki, dangane kuma abin da ya faru a daren jiya a Jami’ar Fasaha ta Sharif, ina mai nuna damuwata tare da shawartar jami’an da abin ya shafa da su rika girmama jami’ar gwargwadon iko.