Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

17 Satumba 2022

05:36:56
1305999

Masanin Portugal

Riko Da Akidar Imam Husaini (AS) Ita Ce Tushen Tafarkin Imam Khumaini Wanda Ya Tabbatar Da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran

"Mohammed Mostahsen" daya daga cikin manajojin majalisar Ahlul-Baiti (AS) ta kasar Portugal ya ce: Riko da akidar Imam Husaini (AS) da kuma tafarkin hadin kai wasu abubuwa ne guda biyu na asasi da Imam Khumaini (RA) ya yi bayaninsu kuma yayi riko da su.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - an gudanar da wani taron tattaunawa na kasa da kasa a Karbala a bisa jagorancin da cibiyar "Arbaeen International Foundation".

 

A wannan taro da aka gudanar tare da hadin gwiwar jami'ar Al-Hussein (AS) da kuma kungiyar malaman jami'ar Iraki (Reshen Karbala) sun gabatar da mahawararsu.

 

Malam "Muhammad Mustahsen" daya daga cikin manajojin "Majalisar Ahlul-Baiti (A) ta Portugal" na daya daga cikin masu tunani da suka halarci wannan taron, wanda ya gabatar da jawabi kan "dangantakar yunkurin Ashura da tsarin dimokuradiyya na addini".

 

 Abin da ke tafe shi ne zabnabun kalamansa ne a cikin taron karawa juna sanin:

 

-Ziyaar Arbaeen na Husaini abu na gaskiya da ba za a iya gudanar da shi ba sai da kulawar Imam Asr (AS).

 

- A yau miliyoyin mutane daga kasar Iraki da kasashe daban-daban ne ke yin tattaki zuwa Karbala. Da yawa daga cikinsu sun fara tafiyar da kafafuwansu zuwa Karbala.

 

- Karbala kasa ce ta Imam Husaini (a.s.) kuma aikin ziyarar na yau yana da nasaba da sadaukarwar shahidi "Abu Mahdi Al-Muhandis" da shahidan janar "Suleimani" da dubban shahidai.

 

- Tsarin Dimokuradiyya na Addinin Musulunci, haƙiƙa ce kuma gaskiya. Da a wasu lokuta ana iya kafa irin wannan tsarin kuma wani lokacin ba zai yiwu ba.

 

- Abin da ke da muhimmanci a yanzu shi ne wanzuwar tsarin dimokuradiyyar Musulunci, wato Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

 

- Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta tsaya tsayin daka kan dukkan makiya tun farkon kafuwarta. Wannan tsarin, wanda ya kasance toho tun farko, ya rikide ya zama bishiya mai tsayi a yau kuma ya kai matsayin da ya dace.

 

Tabbas ya kamata mu lura cewa idan muka ce tsarin Jamhuriyar Musulunci tsari ne na kwarai, ba yana nufin tsarin siyasa a dukkanin kasashen musulmi ya kasance kamar wannan tsarin ba.

 

- Tsarin siyasar demokradiyya na iya bambanta a kasashe daban-daban. Abin da ke da mahimmanci shi ne bin ƙa'idodi.

 

- Imam Khumaini (RA) ya zabi tsarin dimokuradiyyar Musulunci ne ta hanyar riko da ka'idoji.

 

Riko da akidar Imam Husaini (a.s.) da kuma tafarkin hadin kai, abubuwa ne guda biyu na asasi da Imam ya bayyana da kuma riko da su.

 

- A yau wannan kokari na Imam Khumaini (RA) ya samu kyakykyawan hanya da bunkasa a karkashin jagorancin Jagoran juyin juya halin Musulunci Sayyid Ali Khamanee Dz da Ayatollah Sistani.

 

-Aikinmu shi ne bin tafarkin Imam Hussain (AS) a karkashin jagorancin maraji’an addini da taken "Lallai Hussain Shi Ke Tattara Mu " da "Labbaik Ya Hussain".

 

- Husainiyawa ba su da iyaka na kasa. Al’umma daya ne a karkashin tuta daya. Mu duka Husaini ne kuma Dole ne mu yi aiki tare don tabbatar da mafarkin “Al’umma Daya”

Hujjat-ul-Islam Wal Muslimin "Syed Ziauddin Al-Safi", farfesa "Abdulamir Al-Quraishi", shugaban Cibiyar Nazarin Musulunci ta Imam Husaini (AS), Hujjat-ul-Islam Wal -Muslimin "Hamid Ahmadi", shugaban kwamitin al'adu da ilimi na hedkwatar Arbain, Dr. "Nasser Sudani", shugaban jami'ar Amirul Momineen ta Ahwaz da wakilin wannan birni a majalisar musulunci da Dr. "Monir al-Daemi" sun kasance fitattun baki a wannan taron na karawa juna sani.