Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

23 Agusta 2022

16:53:04
1300333

Amurka Ta Ce Akwai Ci Gaba A Sabon Daftarin Yarjejeniyar Nukiliyar Da Iran Ta Gabatar

Amurka ta musanta cewa tana jan kafa wajen bada amsa game da daftarin da Iran ta gabatar na neman ceto yarjejeniyar nukiliyar 2015.

Da yake sanar da hakian kakakin gwamnmatin Amurka Ned Price, ya ce ba yadda Tehran ke fada ba ne cewa muna jan kafa wajen bayar da amsa, muna nazari ne kan wasu batutuwa masu dan sarkakiya.

Amurkar dai bata fayyace wadanne batutuwa ba ne.

Amma a halin da ake ciki akwai ci gaba fiye da cen baya musamman a daftarin da Iran ta gabatar inda ta janye wasu bukaci da ba ma su yiwuwa ba ne, wanda kuma hakan ya sanya mun kara samun kusantuwa daga cimma yarjejeniya fiye da makwanni biyu da suka wuce inji Ned Price.

‘’Cewar muna jan kafa domin kawo tsaiko wajen cimma yarjejeniya ta ko wane hali ba haka ne inji M. Price, muna kawai nazari ne kan bukatun na Iran, kuma zamu bada amsa da zarar mun gama.

342/