Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

16 Disamba 2021

13:28:12
1209238

Najeriya: Sheikh Zakzaky Ya Yi Allawadai Da Kisan Kiyashin Zariya

Sheikh Ibrahim Zakzaky shugaban kungiyar harka Islamiya ko IMN ta mabiya mazhabar Ahlul baiti (a) ya yi allawadai da kisan kiyashin birnin Zariya wanda ya auku a cikin watan Dicembar shekara ta 2015, wato shekaru 6 da suka gabata. Ya kuma kara da cewa harkar da yake jagoranta tana son samar da farkawa ce dangane da addinin musulunci.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Banda haka shugaban na harka islamiyya a Najeriya ya kara da cewa akwai mummunar manufa wajen daukar harkar da yake jagoranta a matsayin kungiya. Ya kuma bukaci yan jarida su bar kiransa da mabiyansa a matsayin yayan wata kungiya. Ya ce su masu gwagwarmaya ne kawai.

Sheikhin malamin yana magana ne da ‘yan jaridu a dai lokacinda ake cika shekaru 6 da kisan kiyashin Zariya inda sojoji suka kashe da dama daga cikin mabiyansa sannan wasu da dama suka ji rauni, daga cikin wadanda suka yi shahada har da ‘yayansa guda uku, sannan bayan haka sojojin sun kona gidansa. Bayan tsare shi na tsawon shekaru kimani 6 a tsakiyar wannan shekara ne wata kotu a kaduna ta wanke shi tare da matarsa Malama Zinat daga aikta laifi a lokacin kisan kiyashin na Zariya.

342/