Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

4 Nuwamba 2021

11:43:26
1195426

Iran: IRGC Sun Fitar Da Hotunan Bidiyo Na Arangamar Da Suka Yi Da ‘Yan Fashin Doron Teku Na Amurka

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) sun fitar da cikakken faifan bidiyon arangamar da suka yi a karshen watan da ya gabata, kan wani matakin da Amurka ta dauka na yin fashin teku a kan wani jirgin ruwan Iran.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Lamarin dai ya faru ne a ranar 25 ga watan Oktoba, amma an fitar da labarai da hotunan abin da ya faru a ranar yau Laraba.

Sojojin Amurka sun kwace jirgin ruwan dakon man fetur na kasar Iran a tekun Oman mai matukar muhimmanci, inda suka mika danyen man da yake dauke da shi zuwa wani jirgin ruwa.

Daga nan ne dai rundunar ta IRGC ta kai farmaki kan jirgin ruwa na biyu, inda ta saukar da jiragenta masu saukar ungulu a kan rufinsa, tare da tilasta jirgin ya karkata akalarsa zuwa gabar ruwa ta Iran.

Hotunan sun nuna yadda lamarin ya faru daki-daki, inda da farko ya nuna kwamandan leken asiri na rundunar sojojin ruwa ta IRGC da cibiyar tattara bayanan sirri da ke gano jirgin ruwan da aka sace.

Daga baya an ga rundunar sojojin ruwa ta IRGC tana aikewa da na'urori da makamai domin daukar matakin gaggawa zuwa yankin, domin kwace kayayyakin da Amurka ta yi fashinsu.

Daga nan sai dakarun kwamandojin suka gudanar da wani samame da jirgi mai saukar ungulu, wanda ya sauka a kan jirgi na biyu, tare da kwato kayan da aka sace.

A halin da ake ciki, ana ganin rukunin jiragen ruwa marasa matuki na IRGC Navy, jiragen ruwa masu matsanancin gudu, da sauran jiragen ruwa suna taimakawa wajen kammala aikin.

342/