Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : IQNA
Alhamis

29 Yuli 2021

14:42:04
1164477

Kotu A Kaduna Ta Wanke Sheikh Ibrahim Zakzaky Da Maidakinsa

Babbar kotun Kaduna da ke sauraren shari’ar Sheikh Ibrahim Zakzaky ta wanke daga dukkanin tuhumce-tuhumcen da ake yi masa.

ABNA24 : Babbar kotun Kaduna da ke sauraren shari’ar Sheikh Ibrahim Zakzaky jagoran Harka Islamiyya a Najeriya, da maidakinsa Malama Zinat Ibrahim, ta wanke su daga dukkanin tuhumce-tuhumcen da ake yi musu.

A zaman da kotu ta gudanar a yau domin ci gaba da sauraren shari’ar, alkalin kotun ya bi dukkanin abubuwan da aka gabatar daya bayan daya, inda ya fara yanke hukunci a kan tuhumce-tuhumcen da ke kan Malama Zinat har guda 8, ya kuma tabbatar da cewa malama Zinat ba ta aikata wadannan laifuka ba.

Sannan kuma daga bisani aka shiga duba tuhumce-tuhumcen da suke a kan sheikh Ibrahim Zakzaky, inda shi ma dai daga karshe alkalin ya yanke hukuncin cewa Sheikh Zakzaky bai aikata ko daya daga cikin laifukan da ake zarginsa da aikatawa ba, kuma ya bayar da umarnin a sake shi.

An kwashe kimanin shekaru ana sauraren wannan shari’a a Kaduna, inda lauyoyin suka gabata bayanai daban-daban domin tabbatar da zarge-zargen da ake yi wa malamin da mai dakinsa, inda a yau ranar 28 ga watan Yuli shekara ta 2021 wannan shari’a ta zo karshe .

342/