Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

16 Mayu 2021

18:11:39
1141577

Isra’ila Ta Wargaza Ginin Tashar Al’Jazeera Da Kamfanin AP A Gaza

Sojojin Isra’ila, sun rusa wani ginin tashar talabijin ta Al’jazeera mallakin Qatar da kuma kamfanin dilancin labaren Amurka na AP, dake yankin Gaza.

ABNA24 : Ginin mai hawa 13 wanda ya kushi ofosohin ‘yan jarida da dama an rusa shi ne ta hanyar harin jiragen sama jin kadan bayan sanar da mai ginin cewa kowa ya yi ta kan shi.

Shugaban kamfanin dilancin labaren na AP, ya fitar da wata sanarawa inda ya sun tsorata da kuma jin mamaki da matakin na Isra’ila

Ita kuwa tashar Al’jazeera tir ta yi da harin, tana mai cewa hakan ba zai sanya ta yin shiru ba game bayana abubuwan dake faruwa a yankin.

Daga bisani dai an rawaito sojojin Isra’ila na cewa, sun kai harin ne saboda ana ajiye kayan soji a ciki.

342/