Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Talata

11 Mayu 2021

13:31:26
1140021

Hamas Ta Yi Wa Isra’ila Ruwan Rokoki

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta kaddamar da wasu jerin hare haren rokoki kan wasu cibiyoyin Isra’ila.

ABNA24 : Hamas ta ce, ta kaddamar da hare haren ne biyo bayan cikar wa’adin data dibarwa dakarun Isra’ila na su janye daga gabashin birnin Kudus da harabar Masallacin na Kudus.

Birgediya Izz ad-Din al-Qassam, na kungiyar Hamas, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa hare haren rokokin ramuwar gayya ne ga “laifuffukan Isra’ila da cin zarafin da Isra’ila ke aikatawa a birnin Kudus.

Ya kara da cewa wannan sako ne da ya kamata makiya su fahimta sosai.

Saidai daga bisani Isra’ila ta kai wasu hare haren sama kan Gaza, inda mutane kimanin ashirin suka rasa rayukansu.

Bayanai sun ce kimanin 19 suka mutu a harin na Isra’ila, ciki har da yara 9.

Kafin hakan dai sama da Falasdinawa 300 ne aka rawaito sun jikkata, a ci gaba da farmakin da ‘yan sandan Isra’ila ke kaiwa kan masu ibada a masallacin na Kudus.

342/