ABNA24 : Sahafin yanar gizo na labarai na ‘Africa news’ ya nakalto Samia Hassan ta na cewa lokaci ya yi wanda mutanen kasar Tanzania za su manta da bambance bambance da ke tsakaninstu don ci gaban kasar Tanzania kamar yadda marigayi shugaba Magufuli yake so.
Samia Hassan dai ta fito ne daga tsibirin Zanzigar na kasar Tanzania. Sannan ta zama mataimakiyar shugaban kasa ne a shekara 2015, sannan an sake zabensu a shekarar da ta gabata.
A halin yanzu dai Samia zata ci gaba da rike wannan matsayin har zuwa shekara ta 2025. Samia Hassan ta bada sanarwar makoki na kwanaki 21, sannan hutu a ranar 21 ga watan Maris da muke ciki, wato ranar da za’a yi masa jana’iza.
Kafin haka dai an daina ganin Magufuli na kimanin makonnin uku kafin a bada sanarwan rasuwansa, kuma har yanzun ba’a bayyana dalilin rasuwarsa ba.
342/