1 Janairu 2020 - 05:25
Turkiyya : An Cafke Mutane 147 Kan Alaka Da Kungiyar (IS)

Rahotanni daga Turkiyya na cewa, an cafke mutane 147 bisa zarginsu da alaka da kungiyar ‘yan ta’adda ta (IS), a wani samame da jami’an tsaron kasar suka kai gabanin bukukuwan sabuwar shekara.

(ABNA24.com) Rahotanni daga Turkiyya na cewa, an cafke mutane 147 bisa zarginsu da alaka da kungiyar ‘yan ta’adda ta (IS), a wani samame da jami’an tsaron kasar suka kai gabanin bukukuwan sabuwar shekara.

Daga cikin wadanda a kama da akwai ‘yan Iraki sama da 40 da kuma wasu gomman ‘yan Syria da kuma wani da asalin kasar Morocco, kamar yadda kamfanin dilancin labaren Anatoli ya rawaito.

An cafke mutanan ne a cikin kwanakin nan a birane shida da suka hada da Ankara, Bursa dake arewa maso yammacin kasar da kuma Batman dake kudu maso gabashin kasar.

Bugu da kari labarin ya ce an kwato tarin bindigogi da harsashai a gidajen da aka kai samamen, a yayin da kuma ‘yan sanda ke ci gaba da farautar wasu mutane 17 a birnin Ankara.

Kasar Turkiya ta fuskanci hare haren ta’addanci da dama a shekarun baya, ciki har da wanda ya ci rayukan mutane 39 galibi ‘yan kasashen waje, wanda kuma kungiyar IS ta dauki alhakinsa.



/129