(ABNA24.com) A wata wasika da shugaban kasar Iran Hassan Rohani ya aikewa shugaban cocin Roman katolika na duniya Paparoma Francis ya taya shi murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Isa ( As ) da kuma sabuwar shekara ta miladiyya. Ya kara da cewa Isa Almsihu annabin ne da ya zo da sakon na zaman lafiya da alheri, kuma ya yi kira zuwa ga yanci ga dukkan dan Adam.
Har ila yau ya yi fatan mabiyar annabi Isa na gaskiya za su bi sauran takwarorinsu mabiya addinai da aka saukar daga sama wajen hakuri da juna da bayar da gudunmawa wajen tabbatar da Adalaci da zaman lafiya a duniya baki daya.
A bangare guda kuma a cikin wani bayani da ya fitar game da ranar Kirsimeti paparoma Francis ya yi kira ga mabiya addinin kirisrta da ka da su bari matsalolin da ke faruwa a coci su nisantar da su daga kaunar ubangiji, ya ce Allah yana son mu baki daya.
Ita dai cocin katolika yayi fama da matsaloli da suka hada da cin zarafin yara kanana ta hanyar yin lalata da su a yan shekarun nan , inda ya nuna cewa daga yanzu ba za’a sake kyale wanda ya ci zarafin wani yaro ba, ko me matsayinsa a coci.
/129
26 Disamba 2019 - 06:45
Lambar labari: 996575
A wata wasika da shugaban kasar Iran Hassan Rohani ya aikewa shugaban cocin Roman katolika na duniya Paparoma Francis ya taya shi murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Isa ( As ) da kuma sabuwar shekara ta miladiyya. Ya kara da cewa Isa Almsihu annabin ne da ya zo da sakon na zaman lafiya da alheri, kuma ya yi kira zuwa ga yanci ga dukkan dan Adam.