6 Nuwamba 2019 - 15:24
​Iran Tana Shirin Tura Iskar Gas Cikin Bututan Tache Yuranium Na Fordow

Hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran ta bada sanarwan cewa a tsakiyar daren yau Laraba ne zata fara tura iskar gas wacce zata gasa sinadarin yuranium a cibiyar tashe makamashin da ke Fordow kusa da birnin Qom a tsakiyar kasar.

ABNA: Hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran ta bada sanarwan cewa a tsakiyar daren yau Laraba ne zata fara tura iskar gas wacce zata gasa sinadarin yuranium a cibiyar tashe makamashin da ke Fordow kusa da birnin Qom a tsakiyar kasar.

Tashar talabijin ta Presstv daga nan Tehran ta nakalto Behrouz Kamalvandi kakakin hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran yana fadar haka a safiyar yau Laraba.

Wannan dai shi ne mataki na 4 wanda kasar Iran take dauka na jingine yarjejeniyar Nukliyar kasar ta shekara ta 2015, saboda ficewar Amurka daga cikin yerjejeniyar, da kuma gazawar kasashen turai wajen cika alkawulla guda 11 da suka amince zasu aiwatar bayan ficewar Amurka daga yerjejeniyar.

A shirin jingine yerjejeniyar mataki na 4 dai, akwai bututan tashe sinadarin Yuranium masu nauyin kilogram 2,800, dauke da sinadarin yuranium mai nauyin kilogram 2000 wanda za’a fara gasasu a tsakiyan daren yau.

Labarin ya kammala da cewa Iran tana dukkan wadannan matakan ne a gaban idon hukumar IAEA mai kula da makamashin nukliya ta duniya, sannan tana daukan matakan ne don tabbatar da cewa sauran kasashen da abin ya shafa sun sauke nauyin da yake kansu dangane da yerjejeniyar ta 2015.

............

300