Ganawa da manyan jami'an Pakistan da rattaba hannu kan takardun hadin gwiwa na daga cikin shirye-shiryen ziyarar ta kwanaki biyu da shugaban ya kai Pakistan. Ministocin masana'antu, ma'adinai da kasuwanci, harkokin waje, tsaro, hanyoyi da raya birane, da gwamnan Sistan da Baluchestan ne suka raka shugaban kasar a wannan tafiya.

2 Agusta 2025 - 19:10
Source: ABNA24

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbayt (AS) - ABNA – ya bayar da rahotan cewa: Shugaban kasar Iran Dr. Masoud Pezhakian ya isa birnin Lahore a yau Asabar (02 Ogustaa 2025) bisa gayyatar da firaministan Pakistan Shahbaz Sharif ya yi masa. Ganawa da manyan jami'an Pakistan da rattaba hannu kan takardun hadin gwiwa na daga cikin shirye-shiryen ziyarar ta kwanaki biyu da shugaban ya kai Pakistan. Ministocin masana'antu, ma'adinai da kasuwanci, harkokin waje, tsaro, hanyoyi da raya birane, da gwamnan Sistan da Baluchestan ne suka raka shugaban kasar a wannan tafiya.

Hoto: Gidan Yanar Gizon Shugaban Kasa

Your Comment

You are replying to: .
captcha