3 Agusta 2025 - 00:03
Source: ABNA24
Saraya Al-Quds Ta Fitar Da Faifan Bidiyo Na Sojan Isra'ila Da Aka Yi Garkuwa Da Su Kafin A Rasa Sadarwa Da Shi

Dakarun Saraya Al-Quds, reshen sojojin kungiyar Jihad Islami, ta fitar da faifan bidiyon da ta ce shi ne hoton bidiyo na karshe na sojan Isra'ila Rom Barslavsky da aka yi garkuwa da shi, kafin a rasa sadarwa da shi da wadanda suke tsare da shi, sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai a wani yanki na zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbayt (AS) - ABNA – ya habarta cewa: Rundunar Quds, reshen kungiyar Jihadil Islami, ta fitar da faifan bidiyon da ta ce shi ne bidiyo na karshe na sojan Isra'ila Rom Barslavsky da aka yi garkuwa da shi kafin a rasa saduwa da shi da, sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai a wani yanki na zirin Gaza.

Barslavsky ya bayyana a fili a cikin faifan bidiyo, sakamakon mummunan kawanya da yunwa da "Isra'ila" ta kakabawa wa Gaza, wanda kuma ya shafi sojojin Isra'ila da aka kama.

Dan Isra'ila da aka kama ya yi kakkausar suka ga gwamnatin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da kuma sojojin Isra'ila, inda ya dora masu alhakin yunwa da tabarbarewar lafiyarsa.

Ya ce, “Netanyahu ne ke da alhakin rashin lafiyata da zubar da jinina.”

Rundunar Al-Quds ta ce an samu faifan bidiyon ne kafin a rasa samun sadarwa da shi. An watsa shi cikin Larabci da Yahudanci, wanda ke nuna sojan da ke kallon yadda Al Jazeera ta ke watsa mugayen abubuwan da Isra’ila take aikatawa akan yara Falasdinawa da ke fama da yunwa a Gaza.

A cikin roƙonsa, sojan ya ce, “Ina mutuwa a nan… ku kawo abinci,” ya bayyana hakan cikin kuka, yana roƙon a kai masa abinci.

Ya kara da cewa, "Ni soja ne kuma da kyar nake cin abinci... Ina gab da mutuwa, kuma ina da yakinin cewa zan samu lahani na dindindin na jiki da na hankali."

Barslavsky ya kara da cewa tun bayan harin da Isra'ila ta kai na baya-bayan nan, an bar shi ba tare da samun abinci ko ruwa ba, "Na shafe watanni hudu ina cikin kabari, ina rayuwa a cikin jahannama da wahala."

Your Comment

You are replying to: .
captcha