Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbayt (AS) - ABNA – ya bayar da rahotan cewa: Bayan fitar da wani fayil na faifan bidiyo da dakarun Qassam suka yi game da wani fursuna na Isra'ila a Gaza, dubun-dubatar yahudawan sahyoniya sun gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a birnin Tel Aviv, inda suka bukaci a gaggauta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni.
A gefen zanga-zangar, an nuna hotunan wani fursuna na Isra'ila a Gaza, wanda ya yi rauni sosai kuma yana cikin wani yanayi mai muni sakamakon yunwa da fatara.
Your Comment