Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbayt (AS) - ABNA – ya habarta cewa: dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) sun fitar da sanarwar tunawa da zagayowar ranar shahadar Isma'il Haniyah, tsohon shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas, tare da jaddada cewa tsayin dakan da al'ummar Gaza suka yi na fuskantar kisan kare dangi na ta’addancin gwamnatin sahyoniyawa na nuni da cika alkawarinsu ga manufofin gwagwarmayar 'yantar da Falasdinu da Quds da ci gaba da gwagwarmayar shahidan Palasdinawa cikinsu har da Shahid Haniyah.
Sanarwar ta bayyana cewa, hana al'ummar Gaza samun kayan masarufi kamar ruwa, abinci, da magunguna ya zama take hakkin bil'adama da dokokin kasa da kasa, kuma yana iya zama wani sabon salo na kisan kiyashi. IRGC ta jaddada cewa wannan laifi ya sha Allah wadai a duniya, duk kuwa da irin goyon bayan da wasu kasashen yammacin duniya suke yi.
Har ila yau IRGC ta yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa Shahid Haniyya a birnin Tehran tare da bayyana cewa, guguwar Al-Aqsa ba lamari ne na tarihi kawai ba, sai dai dabara ce ta aiki bisa sadaukarwar shahidai don tantance makomar Palastinu. Sanarwar ta yi watsi da matakin kafa kasashe biyu tare da sake nanata taken Hamas: Ba Za Mu Amince Da Isra'ila Ba.
Bugu da kari, IRGC ta yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi a Gaza da kuma shirun da hukumomin kasa da kasa suka yi, tana mai cewa kakaba yunwa da gangan laifi ne kan bil'adama kuma laifin yaki ne. Sun yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su kawo karshen kawanyar Gaza, da sanya takunkumi mai tsauri kan gwamnatin sahyoniyawa, tare da gurfanar da wadanda suka aikata wannan laifi a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya.
Bayanin ya karkare da imanin cewa, wannan shiri na kisan kare dangi na da nufin karbe ikon yankin mai dimbin arziki, Amma tare da goyon bayan hadin kan duniya da kuma zanga-zangar kasashen duniya, akwai fatan gwamnatin Sahayoniya da Amurka za ta wargaje.
Your Comment