(ABNA24.com) A wani taron hadin guiwa karo na 4 da ya guna tsakanin kasar Iran da kasar Afrika ta kudu a nan birnin Tehran ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Jawad Zarif ya jaddada game da kyakkyawar dangantarkar siyasa da mahanga ta bai daya da kasashen suke da shi , da ya shafi yankin da ma duniya baki daya, da suka hada da batun Palasdinu da kare hakkin bil adama da sauran batutuwa daban daban,
Har ila yau zarif ya nuna fatansa na ganin an kara fadada dangantaka tsakanin kasashen biyu, a bangaren gwamnati da masu zaman kansu, tare da yin aiki tare a fagagen tattalin arzikikasuwanci, llimi da kimiya da fasaha
Da yake ishara game da tattaunawar Iran da kasashen 5 na turai kan shirin ta na Nukiliya na zaman lafiya, ya bayyana cewa ficewar Amurka rana tsaka keta kudirinkwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya mai lamba 2231ne, da sabawa bukatun dukkan mambobin Majalisar, kuma ya gurgunta yunkurin da ake yi na warware batun ta hanyar diplomasiya da bangarorin suka yi amanna da shi.
/129