14 Oktoba 2019 - 05:10
​Jagora Juyin Musulunci Na Iran Ya Bukaci Dakarun IRGC Da Su Kara Zama Cikin Shiri

A lokacin bukin yaye daliban jami’ar soji ta Imam Hussaini dake nan birnin Tehrana yau Lahadi,jagoran juyin juyin musulunci na Iran Ayatullah sayyid Ali khanma’i,ya fadi cewamugun nufi dakasar Amurka take nunawa dakarun kare juyin musulunci a iran , ya kara musu mutunci , kumamun godewa Allah a yau dakarun na IRGCs suna da kima da mutunci a ciki da wajen kasa.

(ABNA24.com) A lokacin bukin yaye daliban jami’ar soji ta Imam Hussaini dake nan birnin Tehrana yau Lahadi,jagoran juyin juyin musulunci na Iran Ayatullah sayyid Ali khanma’i,ya fadi cewamugun nufi dakasar Amurka take nunawa dakarun kare juyin musulunci a iran , ya kara musu mutunci , kumamun godewa Allah a yau dakarun na IRGCs suna da kima da mutunci a ciki da wajen kasa.

Kasar Amurka dai ta sanya dakarun kare juyin cikin jerin sunayen kungiyoyin yan ta’adda a duniya a watan Aprilun da ya gabata.

Har ila yau jagoran ya bayyana cewa babban darasin da dakarun za su koya kamar yadda yazo aya ta 60 ta cikin suratul Anfal inda Allah yake cewa “ku yi musu tanadi da dukkan karfinku da kuma tanadi da dawakai ku rika tsoratar da makiyan Allah kuma makiyanku” , daga karshe jagoran ya ce wannan ayar tana nufin bukatar ku kara karfinku gwargwadon iko, ta hanyar kafa kungiyoyi masu karfi da karko.





/129