(ABNA24.com) Bijan Namdar Zanganeh ministan kula da manfetur na kasar Iran ya caccaki kasar saudiya game da kara bankama harin da dakarun sojin kasar Yamen sukakai a kamfanin samar da manfeturdin kasa na Aramco a ranar 14 ga watan satumbadomin cimma wasu manufofin siyasa, duk da sanar da alhakin kai harin da kungiyar huthi ta kasar Yamen ta yi.
Ya kara da cewa tun da farad a gangan kasar saudiya ta bankama batun harin da aka kai, domin cimma wasu manufofin siyasa, amma a hakikanin gaskiya lamarin bai kai haka ba,
Daga karshe ministan albarkatun man na kasar Iran ya kore zargin da Saudiya ta yi na hannun kasarsa a kai harin da nufin kawo cikas game da ayyukan hako mai da take yi domin ta siyar da nata man da take fuskantartarnaki tun bayan da kasar Amurka ta kakaba mata takunkumin hana siyan man feturi din kasar.inda yabayyana cewa harin bashi da wata alaka ko kadan game da ayyukan fitar da manfetur da iran din take yi.
/129
1 Oktoba 2019 - 04:34
News ID: 979453

Bijan Namdar Zanganeh ministan kula da manfetur na kasar Iran ya caccaki kasar saudiya game da kara bankama harin da dakarun sojin kasar Yamen sukakai a kamfanin samar da manfeturdin kasa na Aramco a ranar 14 ga watan