(ABNA24.com) A jiya musulmi ‘yan gudun hijirar Rohingya a kasar Bangaladesh sun bukaci hakkokinsu da hakan ya hada ba su hakkokinsu na ‘yan kasa a Myanmar.
Bayanin ya ce adadin wadanda suka taru ya kai kimanin mutane dubu uku da 400 a cikin wani sansanin da aka tsugunnar da su a cikin kasar Bangaladesh.
A lokutan baya gwamnatin kasar Bangaladesh ta bukaci ‘yan kabilar Rohingya da suke gudun hijira a kasar da su koma kasarsu Myanmar don kashin kansu ga duk mai son ya koma, ba tare da wani tilasci ba, amma babu wanda ya yarda ya koma.
A cikin shekara ta 2017 ce sojojin gwamain Myanmar suka kaddamar da hare-hare a kan lardin Rakhin wanda ‘yan kabilar Rohingya musulmi suke zaune a cikinsa, inda suka kashe dubban musulmi da kuma kone gidajensu da makarantunsu da masallatansu, lamarin da ya tilasta dubban dauruwa tserewa zuwa kasar Bangaladesh.
/129