(ABNA24.com) A safiyar wannan lahadi mataimakin ministan harakokin wajen Iran Abbas Araqchi ya gana da Helga Schmid mataimakiyar Federica Mogherini babbar jami’a mai kula da harakokin siyasar wajen tarayar Turai da kuma wakilan tawagar kasashen China da Rasha a gefen taron kasashen da suka rage a yarjejeniyar nukiliyar Iran da ya gudana a birnin Vienna, na kasar Austiriya, a kebance.
Kafin shiga taron, Sayyid Abass Aragchi ya tattauna da bangarorinne a kebance kan abubuwan da suka faru cikin watan da ya gabata, musaman ma kan matakin da kasar Iran ta dauka na jingije wani bangare na yarjejeniyar nukiyar da ta cimma tare da kasashen 5 gami da kasar Jamus a shekarar 2015, da komawar Amurka a Hukumar dake kula da makamashin nukiya, da kuma rike jirgin dagon man Iran da kasar Birtaniya ta yi a mashigar ruwa ta Jabalul Tariq.
Araghchi ya ce rike jirgin dagon man Iran da kasar Birtaniya ta yi a mashigar ruwa ta Jabalul Tariq ya sabawa yarjejeniyar nukiliyar da kasar Iran ta cimma tare da manyan kasashen Duniya, a ganinmu bai kamata ba kasar dake cikin wannan yarjejeniya ta samar da shinge na hana fitar man kasar Iran zuwa wata kasar ba, wannan ya sabawa yarjejeniyar.
Har’ila yau mataimakin ministan harkokin wajen kasar ta Iraqi, bayan kammala taron wakilan yerjejeniyar ta Iran ya ce angudanar da tattaunawa mai kyau amma matsalarmu a ko yaushe it ace aiwatarwa.
/129
29 Yuli 2019 - 03:52
Lambar labari: 965479
A safiyar wannan lahadi mataimakin ministan harakokin wajen Iran Abbas Araqchi ya gana da Helga Schmid mataimakiyar Federica Mogherini babbar jami’a mai kula da harakokin siyasar wajen tarayar Turai da kuma wakilan tawagar ...