27 Yuli 2019 - 06:28
Nijar : Mutane 147 Aka Sace Cikin Watan Yuni A Diffa

Ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD, ya bayyana cewa mutane 147 ne aka yi garkuwa dasu a cikin watan Yuni da ya gabata a jihar Diffa dake Jamhuriya Nijar.

(ABNA24.com) Wannan shi ne adadi mafi girma da aka samu na mutanen da aka sace a jihar ta Diffa mai fama da matsalar Boko Haram dake gabashin jamhuriya ta Nijar, tun bayan shekara 2015.

Ana dai danganta sace sacen mutanen ga kungiyar nan da akafi sani da Boko haram, da rassamta da suka balle, wandanda har yanzu suke ci gaba da zama babbar barazana ga kasahen dake yankin tafkin Chadi.

A cewar wani bayyani da wakilin musamman na MDD, kan AFrika ta yamma da yankin Sahel, Mohamed Ibn Chambas, an samu dan sukuni game da halin da ake ciki a yankin inda matsalar tsaro ta haifar da tabarbarewar al’amuran jin kai wanda ba’a taba ganin irinsa ba a yankin, inda mutane miliyan 5,1 daga kasashen Burkina Faso, Nijar, Mali ke cikin bukatar agaji.

Jami’in ya kara da cewa, idan yanayin tsaro da jin kai, ya kasance mafi muni a kasashen Mali da Burkina faso, a NIjar ma lamarin yana daukar hankali.

Jihar Diffa dake gabashin Nijar, wacce ke karkashin dokar ta baci tun cikin shekara 2015, na mai fama da matsalar mayakan Boko haram, da kuma kwararar ‘yan gudun hijira daga Najeriya da wasu sassa na yankin, amma a baya bayan nan matsalar garkuwa da mutane don neman kudin fansa, ita ta addabi jihar ta Diffa.





/129