(ABNA24.com) Karamin ministan sharia’a a kasar Britania kuma dan jam’iyyar Labor ya bayyana cewa bai kamata kasar Britaniya ta zama dan koren kasar Amurka ba.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto Richard Borgon yana fadar haka a jiya Lahadi, ya kuma kara da cewa yakamata gwamnatin kasar Britania ta sassauta rigimar da ta shiga da kasar Iran kan tsare jiragen ruwan juna da suke yi.
A farkon wannan watan ne sojojin kasar Britania suka tsare kataparen jirgin dakon man fetur mai suna Grace 1 mallakin kasar Iran a kusa da tsibirin Jabal Tariq, sannan daga baya ita ma kasar Iran ta tsare wani jirgin ruwa mallakin kasar ta Britania saboda sabawa dokokin tukin jiragen ruwa a mashigar ruwa ta Hurmuz.
Daga karshe Richard Borgon ya yi kira ga gwamnatin kasar Britania kada ta zama mai bin muradun kasar Amurka ido a rufe.
/129
23 Yuli 2019 - 04:20
Lambar labari: 963582
Karamin ministan sharia’a a kasar Britania kuma dan jam’iyyar Labor ya bayyana cewa bai kamata kasar Britaniya ta zama dan koren kasar Amurka ba.