31 Janairu 2019 - 19:36
Nageria: Jam'iyar APC Bata Da Dan Takara A Zamfara

Hukumar Zabe a Najeriya ta ce tana kan matsayinta na babu dan takarar gwamna na jam'iyyar APC mai mulki a jihar Zamfar

Jaridar Premium Times ta Najeriya ta nakalto wani kwamishinan zabe mai suna Festus Okoye yana fadar haka a jiya Laraba ya kuma kara da cewa kotuna guda biyu ne suka yanke hukunci dangane da zaben fidda gwani na cikin jam'iyyar APC a jihar Zamfara. Inda kotun da ke jihar ta ce an yi zabe, a yayinda wata babban kotu a abuja ta ce an gudanar da zaben amma ba mai inganci ba. 

Don haka kwamishinan zaben ya jam'iyyar APC bata da dantakar gwamna na na majalisun jihohi da kuma na tarayyar a zaben da za'a gudanar a nan gaba a cikin wannan shekara.

Har'ila yau hukumar zaben ta fidda sunayen dukkan yan takarar da ta amince da su tsaya takara a zabubbuka na ranar 16 ga watan Febreru da kuma 2 ga watan Maris na wannan shekara.