Cikin wata sanarwa da ta fitar, Ma’aikatar Tsaron Nijar ta ce, an kashe mayakan ne a wani aikin kakkabe su da aka fara gudanarwa a ranar Jumma’ar da ta gabata a kusa da kogin Komadugu da ya raba Nijar da Najeriya.
Sanarwar ta kara da cewa, an kuma raba mayakan na Boko Haram sama da 200 da makamansu.
Kungiyar Boko Haram ta shafe tsawon shekaru tana kaddamar da farmaki kan kasashen Nijar da Najeriya da Chadi da Kamaru, yayin da a cikin watan Yulin shekarar 2016, ta kashe sojojin Nijar fiye da 30 a garin Bosso, abin da ya sa Chadi ta aika da sojoji dubu 2 don taimakawa kasar a wannan yaki.