Rahotanni na cewa, mayakan sun tsallako ne daga makwabciyar kasar, wato Najeriya, in da suka dirar wa garin Assigashia na Kamaru a cikin daren ranar Talata.
Garin Assigashia wanda ke kan iyaka da Najeriya ya yi fama da kutsen mayakan Boko Haram a can baya.
Akalla fararen hula da sojoji dubu 2 ne kungiyar ta kashe a Kamaru bayan gwamnatin kasar ta shiga yaki da mayakanta a shekarar 2014.
A bangare guda, wasu rahotannin daga birnin N’djamaina na Chadi na cewa sojin kasar biyu ne suka gamu da ajalinsu sakamakon kwanton bauna da mayakan na kungiyar Boko Haram suka kai musu a wani yanki da ke dab da kan iyakar Najeriya.