Jaridar Punch ta Nigeria ta nakalto Ma'aikatar man fetur ta Nigeria tana bayyana haka a jiya Alhamis, bayan wata ziyarar aiki wacce wata tawagar ma'aikatar, karkashin jagorancin karamin ministan man fetur na Nigeria Emmanuel Ibe Kachikwu ta kai jumhuriyar Niger a ranar Laraban da ta gabata. Ma'aikatar ta bada wannan labarin ne a shafinta na tweeter a jiya Alhamis ta kuma kara da cewa tawagar ministan ta hadu da shugaba Mohammad Yusuf inda suka cimma fahintar juna kan wannan aikin wanda zai amfani kasashen biyu.
Lararin ya kara da cewa bangarorin biyu zasu rattaba hannun kan cekekken takardun gudanar da wannan gagarumin aiki, tare da bayyan filla-filla yadda aikin zai kasance a cikin yan kwanaki masu zuwa. Har'ila yau labarin ya kara da cewa matatan man zata kasance cikin jihar katsina kusa da kan iyakar kasashen biyu.