'Yar kunar bakin wanke ta farko ta tayar da bam din da ke jikinta ne a cikin kasuwar Biu "layin 'yan manja da doya," a cewar wani wanda ya shaida al'amarin.
Sai dai 'yar kunar bakin ta biyu ta ta da bam din da ke jikinta a kusa da kasuwar, wadda take ci a ranar Asabar.
Kakakin rundunar sandan jihar Borno DSP Isuku Victor ya tabbatarwa aukuwar harin, inda ya ce 'yan kunar bakin waken sun kai harin ne da misalin karfe 11:40 na safe a ranar Asabar.
Ya ce bayan mutanen da suka rasa rayukansu, akwai wadansu mutum 53 da suka jikkata.