Birgediya Janar Amir Hatami, Ministan tsaron na Iran, ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da yake mayar da martani ga barazanar ta Trump inda ya ce dakarun IRGC din dai suna daga cikin dakarun da suke sahun gaba wajen fada da ta'addanci, don haka duk wani kokari na bata sunansu ba abin da zai haifar face taimakon yaduwar ayyukan ta'addanci.
Har ila yau ministan tsaron na Iran ya sake jaddada aniyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na fuskantar duk wata barazanar Amurka, yana mai cewa dakarun kare juyin, sojoji da sauran dakarun kasar Iran bakinsu ya zo daya wajen tsayin daka da kuma tinkarar barazana da girman kan Amurka.
A ranar 15 ga watan Oktoban nan ne dai ake sa ran Shugaban Amurkan zai sanar da wasu siyasar gwamnatinsa kan Iran musamman kan yarjejeniyar nukiliya da kuma dakarun kare juyin juya halin Musulunci, lamarin da jami'an Iran suka ce suna nan suna zuba ido kuma za su mayar wa Amurkan da martanin da ya dace.288