Wannan dai na zuwa ne a yayin da Malamin ya cika kwanaki 500 ana tsare da shi ba tare da wani kwakkwaran dalili ba a cewar ta (Islamic Mouvement in Nageria).
Mahalarta gangamin dai sun shiadawa masu aiko da rahotannin cewa, sun fito ne cikin lumana don nuna rashin yardarsu da yadda gwamnatin Shugaba Buhari take ci gaba da nun ahalin ko kula akan kisan kiyashin Zariya da sojoji suka aiwatar bisa umurnin ta.
Kungiyar ta IMN ta ce an kashe mata mabiya sama da dubu daya a cikin kasa da sa'o'i 48 a karshen watan Disamba na shekara 2015.