24 Faburairu 2017 - 16:41
Shekau ya sanar da kashe kakakinsa

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya bayyana kashe mai magana da yawun kungiyar sakamakon yunkurin kifar da shugabancinsa.

A wani faifan bidoyo na tsawon mintuna 50 da kamfanin yada labaran AFP ya ce yana yawo a tsakanin mayakan, Shekau ya ce ya kashe Tasiu wanda ake fi sani da Abu Zinnira saboda shirya masa makarkashiya.

Abu Zinnira ya sha fitowa a fai-fan bidiyon mayakan sanye da kaki da rawani, ciki har da na garkuwa da ‘yan matan Chibok sama da 200 a Afrilun 2014.

Wannan na zuwa ne a yayin da rundunar Sojoyin Najeriya ke ikirarin kakkabe mayakan daga mabuyarsu ta karshe da ke dajin Sambisa a jahar Borno.288