7 Disamba 2016 - 19:20
Sojin Syria Sun Kwace Mafiya Yawan Birnin Aleppo Daga Hannun 'Yan Ta'adda

Sojojin kasar Syria sun kwace yanki na karshe da 'yan tawayen kasar ke rike da shi a tsohon birnin Halab (Aleppo) a ci gaba da shirin da sojojin suke da shi na fatattakan 'yan ta'addan daga arewacin garin na Halab da suke rike da shi tsawon shekaru.

Kungiyar nan mai ikirarin kare hakkokin bil'adama a Siriyan ta Syrian Observatory for Human Rights da ke da helkwata a Birtaniyya sojojin Siriyan sun kwace tsohon birnin na Halab bayan da masu dauke da makamin suke fice daga garin sakamakon ci gaba da wutar da suke fuskanta daga wajen dakarun na Siriyan.

A halin yanzu dai sama da kashi 80 cikin dari na arewacin garin na Halab wanda ya shafe sama da shekaru 4 a hannun masu dauke da makamin a halin yanzu yana hannu sojojin gwamnatin Siriyan ne a yayin da sojojin na Siriya da suke samun dauki kawayensu suke ci gaba da kutsawa da nufin kwace shi gaba daya daga hannun 'yan ta'addan.

'Yan ta'addan dai sun fara kiran da a tsagaita wuta da kuma sasantawa lamarin da da wuya gwamnatin Siriyan ta amince da shi, kamar yadda a jiya ma kasashen Rasha da China suka hau kujeran naki kan wani kuduri da kasashen yammaci suka gabatar a Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya da nufin tsagaita wuta a garin na Halab lamarin da ake ganinsa a matsayin wani kokari ne kawai na sama wa 'yan ta'addan mafiya sakamakon ci gaba da barin wutan da suke fuskanta daga wajen sojojin Siriyan da kawayensu.288