29 Agusta 2016 - 10:18
Yawan Sojojin Gwamnatin Libiya Da Suka Rasa Rayukansu A Gumurzun Garin Sirt Sun Haura Zuwa 34

Yawan sojojin gwamnatin Libiya da suka rasa rayukansu a gumurzun da suke yi na kawo karshen mamayar mayakan kungiyar ta'addanci ta Da'ish a garin Sirt sun haura zuwa 34 tare da jikkatan fiye da 180 na daban.

Majiyar asibiti ta sanar da cewa: A dauki ba dadin da ake ci gaba da yi tsakanin sojojin gwamnatin hadin kan kasar Libiya da mayakan kungiyar ta'addanci ta Da'ish a garin Sirt, sojojin Libiya 34 suka rasa rayukansu a jiya Lahadi, yayin da wasu fiye da 180 suka jikkata.

Rahotonni sun bayyana cewa; Sojojin gwamnatin na Libiya sun doshi tungar karshe na 'yan ta'addan kungiyar ta Da'ish lamarin da ga dukkan alamu karshen mamayar 'yan ta'addan kungiyar Da'ish ga garin Sirt ya yi kusan zuwa karshe.

Sojojin Amurka suna tallafawa sojojin na Libiya ta hanyar kaddamar da hare-hare ta sama kan mayakan kungiyar Da'ish a garin na Sirt amma nakiyoyi da 'yan ta'addan suka bisine a kan hanyoyi suna daga cikin dalilan da suke janyo cikas ga sojojin na Libiya. 288