Frai ministan ya kuma umarci 'yan sanda su gudanar da cikakken bincike kan kisan.
A ranar Juma'a da dare ne aka harbe matar, mai shekara 38, lokacin da take kan hanyarta ta komawa gida a Karachi, a mota, bayan ta gudanar da wani taron karawa juna sani.
Taron da ya kasance kan zargin hannun sojojin Pakistan a azabtarwa da kuma kisan masu fafutukar kare hakkin dan adam na kasar.ABNA