12 Afirilu 2015 - 12:58
Ana jiran sakamakon zaben gwamnoni a Najeriya

Al’ummar Najeriya na sa ran samun sakamakon zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun Jiha a yau Lahadi bayan an kammala jefa kuri’a a Jihohin da aka gudanar da zaben a jiya Assabar.

A Jihohin kasar 29 ne aka gudanar da zaben gwamnoni daga cikin Jihohi 36. Sai dai kuma rahotanni sun nuna cewa mutane ba su fito ba kamar yadda suka fito a zaben shugaban kasa.

Zaben gwamnonin ya haifar da rasa rayuka a wasu yankunan Najeriya da aka samu rikici.

Hukumar Zaben kasar tace ta gamsu da yadda aka gudanar da zaben, duk da wasu rahotanni da ke cewa an yi satar akwatunan zabe a wasu jihohin kasar.

An sami rudani da tashin hankali a wasu jihohin kasar inda rahotanni suka ce har an kashe shugaban jam’iyyar PDP a Jihar Ebonyi.

Sannan an sami tashe tashen hankula a jihohin Imo da Rivers a kuidancin kasar, da kuma Kano da Katsina a arewaci.

Jami’an gwamnatin Jihar Rivers sun zargi wasu jami’an tsaro da hannu a rikicin, kamar yadda Kwamishinar Yada labaru Ibim Semenitari ta shaidawa Rediyo Faransa.

A jihar Katsina ‘yan Sanda sun yi nasarar murkushe yunkurin wasu ‘yan bangar siyasar, da suka yi yunkurin yin awon gaba da kayan zabe a karamar hukumar Dan Musa.

Yanzu dai sakamakon zabukan da yadda ‘yan kasar da ma ‘yan takarar za su karbi sakamakon ne, za su nuna makomar tashe tashen hankulan a wasu yankunan na Najeriya.ABNA