Shugaban Kenyan ya ce a lokacin makokin za'a sauko da tutocin kasar kasa-kasa
Kungiyar bayar da agaji ta Red Cross a Kenyan ta ce ya zuwa yanzu, 'yan-uwa sun gano gawarwakin dalibai 50, a dakin ajiyar gawa dake birnin Nairobi.
Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenyan ya ce hukumomin Tsaro na kasar zasu kara matsa kaimi wajen yaki da kungiyar mayakan al-shabab
Jami'ar Al-Azhar ta birnin alkahira, ta yi allawadai da abinda ta kira harin ta'addanci da aka kai kan dalibai wadanda ba su ji ba , ba su gani ba.ABNA