22 Faburairu 2015 - 09:14
 Maliki Amruka ce ke haddasa duk wata fitina

Noori maliki ayayin da yake kore tuhumar da Obama yake masa na cewar shine ya haddasa duk wata fitina ta kabilancin a Iraki Noori ya furta cewar; sabanin abunda shugaba Obama ke fada Amruka ce ke haddasa duk wata fitine a yanki gabas ta tsakiya musamman Syria da Iraki

Kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaitai{A.S}-ABNA- ya rawaito daga –IRINN- Noori maliki yace kasar Amruka ce ta karfafa yan ta’adda na Da’ish da kuma shigar dasu Iraki da Syria da sauran kasashe.

Ya kara da cewa; hare-haren sama da Amruka ke kaiwa akan Da’ish ba komi bane sai yaudara ya kuma ce; tun farkon fara rikicin Syria Amruka da yan kanzaginta a kudirinsu na kifar da kwamnati Asad, sun taimaka wajan kafa kungiyar Da’ish da da kuma taimakama Alnusra, ta yadda yan ta’adda sukayi karfi a Syria kuma suka yadu a sauran kasashe irin su Iraki, Jodan, Misra, Libiya, da kuma Yeman.ABNA