Shugaba Putin ya sheda wa shugaba Rauhani hakan a wata zantawa da ta hada ta wayar taro a daren jiya, inda shugaban na Rasha ya ce za su ci gaba da yin aiki tare da Iran a dukkanin bangarori, domin kara habbaka tattalin arzikinsu, inda ya ce janye warware takaddama kan shirin Iran na makamashin nukiliya zai taikama wa dukkanin bangarorin Iran da Rasha a cikin mu'amalolinsu na cinikayya da tattalin arziki.
A jiya ne aka kammala zaman tattaunawa tsakanin Iran da manyan kasashen duniya a birnin Vienna na kasar Austria ba tare da cimma yarjejeniya ta karshe ba, amma dukkanin bangarorin sun amince da a ci gaba da tattaunawar domin kai wag a matsaya ta karshe. ABNA