A yau Talata ne aka rantsar da Kafando domin jagorantar kasar har zuwa a gudanar da sabon zaben shugaban kasa bayan hambarar da gwamnatin Blaise Compaore.
Kafin gudanar da bikin rantsuwar, an karrama Kanal Isaac Zida shugaban Soja wanda ya amince ya mika mulki ga farar hula.
A ranar Juma’a ne Kafando zai karbi ragamar tafiyar da Burkina Faso daga hannun Kanala Zida.
Sauyin gwamnati da aka samu a Burkina Faso na zuwa kafin cikar wa’adin kungiyar Tarayyar Afrika, bayan gargadin kakabawa kasar Takunkubi idan har sojoji ba su mika mulki ga Farar hula ba. ABNA