17 Nuwamba 2014 - 07:46

Sojojin kasar Syria sun sami nasarar korar yan ta’adda daga wasu yankunan masu muhimmanci a kusa da babban birnin kasar Damascus.

Tashar telbijin ta Presstv mai watsa shirye shiryenta da harshen turanci a nan Tehran ta bayyana cewa, bayan da sojojin suka kwace garin Mulaiha a ranar 15 ga watan Augustan da ya gabata a ranar asabar da ta gabata kuma ta kori yan ta’adda daga garin Al-Dumayr  wanda yake da nisar kilomita 20 daga birnin Damascus. Kuma yana kan babban titin da ya hada birnin da birnin Bagdaza babban birnin kasar Iraqi.

Banda wannan sojojin kasar ta Syria tare da tallafin mayakan kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon sun sami nasarori masu yawa kan kungiyoyi masu kafirta musulmi a kasar ta Syria wadanda suke gabacin kasar. ABNA