Kera wannan jirgi babban ci gaba ne wajen tsaron kasa kamar yadda babban kwamandan Sojin sama na Iran Janar Amir Ali Haji Zade ya bayyana.
Janar Amir ya kara da cewa kafin karshen wannan shekara za su kera irin wannan jirgi akalla guda 4, kuma a shekaru masu zuwa za su kera irin jirage masu yawa har ma su sayar da su ga wasu kasashe na musulmi.
kasar Iran ta samu kera wannan jirgi ne bayan da ta sabko irinsa kiran kasar Amurka yayin da ya shigo kasar domin leken asiri a shekaru biyu da suka gabata.
Kwararun kasar sun samu nasarar kera wanda ya fi inganci domin sun fadada gudunsa da kuma karfinsa inda yake da damar kai hari bayan leken asiri, yayin da wanda suka kama na kasar Amurka kwa ked a karfin leken asiri kawai ba tare da kai hari ba.ABNA