Bukatar wannan runduna ta musamman dai ya taso saboda yadda yan bindaga daga wasu kungiyoyuin yan ta’adda suka fara wani irin salon yaki na sari ka noke kan sojojin samar da zaman lafiya wadanda komitin tsaron ya aika zuwa arewacin kasar tun farko.
A irin wadan nan hare hare dai sojojin tabbatar da zaman lafiya na majalisar da dama ne suka rasa rayukansu. Kuma aikin rundunar ta musamman a wannan karon zai hada ne da damar shiga tsakanin bangaririn da suke fafatawa da juna a kasar da kuma kare lafiyar sojojin tabbatar da zaman lafiya da ke kasar daga hare haren sari ka noke wanda wasu yan tawayen kasar suka bullo da shi a baya bayan nan.
Kafin wannan bukatar dai komitin Tsaron ta taba tura irin wadan nan rundunar zuwa kasar Democradiyar Congo inda komitan ya bawa rundunar ta musamman damar shiga tsakani don raba fada tsakanin bangarori biyu da kuma shiga fada da duk wani dan tawayen da ya yi taurin kai.
Sauran sojojin samar da zaman lafiya dai basa da wannan hukumin, kuma basa iya shiga cikin yake yaken da ke faruruwa tsakanin bangarori masu adawa da juna.
A makon da ya gabata ne wasu yan bindaga suka kai harin irin na sari ka noke kan sojojin tabbatar da zaman lafiya a kusa da garin Gawo na arewacin kasar wanda ya kai ga mutuwar sojojin kasar Niger guda 9, sannan kafin haka wasu sojojin kasar Senegal dukkaninsu a karjashin sojojin na majalisar dinkin duniya sun rasa rayukansu a wani hari mai kama da shi.
Sai kuma a cikin watan satumban da ya gabata sojojin kasar Chadi 10 ne suka rasa rayuansu a irin wannan harin.
Tun lokacinda sojojin MDD suka fara aikin tabbatar da zaman lafiya a arewacin kasar Mali a cikin watan Jenerun shekara ta 2013M sojoji masu shudin hula 31 suka mutu sanadiyyar hare haren yan bindiga daga wasu kungiyoyin yan tawaye daban daban a arewacin kasar ta Mali.
Banda wannan har yanzun akwai barazanar hare hare daga kungiyoyi dauke da makamai a arewacin kasar kan birnin Bamako babban birnin Kasar.
Rundunar tabbatar da zaman lafiya a arewacin kasar Mali, wanda komitin tsaron ya kafa dai sun fitone daga kasashe 30 na duniya kuma yawansu ya kai sojoji 9,300.
Rundunar mai suna MINUSMA ta karbi ragamar tabbatar da zaman lafiya a arewacin kasar Mali ne a cikin watan jenerun shekara da ta gabata, daga hannun sojojin tarayyar Africa .
Haroo Lodsuse wakilim Majalisar dinkin duniya a kasar ta Mali ya bayyana cewa akwai bukatar kasashe makobta da kasar ta Mali na su bada hadin kai don fuskantar yan ta’ada dauke da makamai wadanda suke kai kawo a kan iyakokin kasashensu.
Wannan ne kadai zai tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a arewacin kasar ta Mali inji shi. ABNA