2 Oktoba 2014 - 09:57
Shugabar Hukumar Tsaron Obama Ta Yi Murabus Saboda Gaza Kare Shi

Shugabar hukumar jami’an tsaro farin kaya da suke da suke da alhakin kare shugaban Amurka da sauran manyan jami’an kasar Julia Pierson ta yi murabus daga mukaminta sakamakon sakaci da aiki da jami’an nata suka yi lamarin da ya sanya ran shugaban Amurka Obaman cikin hatsari.

A jiya Laraba ce dai Julia Pierson din ta sanar da murabus din nata bayan ganawar da ta yi da sakataren tsaron cikin gida na Amurkan Jeh Johnson. Kafin nan dai a ranar talatar da ta gaba, Mrs. Pierson ta shaida wa ‘yan majalisar Amurkan da suka gayyace ta don jin ta bakinta kan wannan gibi da aka samu cewa lalle ta dauki alhakin dukkanin abin da ya farun.

 

Matsalar Julia Pierson, wacce ta dare kujerar shugabancin hukumar jami’an tsaron farin kayan kimanin watanni 18 da suka gabata ta, dai ta faro ne bayan da wani tsohon sojan Amurkan a Iraki dauke da wuka ya tsallake shingen fadar shugaban kasar Amurkan ba tare da jami’an tsaron sun ganshi ba har ya nufi gidan da shugaba Obaman yake kwana kafin a ka gano shi. Wani batun na daban kuma shi ne yadda jami’an tsaro masu gadin shugaban Obama suka gagara dakatar da wani tsohon dan fasa kwabrin makamai kusatar shugaba Obaman da zama tare da shi a cikin na’urar da ke kai mutane sama a dogayen gine-gine alhaki kuwa yana dauke da bindiga a jikinsa.

 

Wadannan abubuwan dai sun sanya jami’an Amurka sukar Mrs Pierson da gazawa wajen tabbatar da tsaron shugaban Amurkan da kiranta da ta yi murabus. ABNA