29 Yuli 2014 - 07:00
Iran:Jagora Musulinci Ya Ce Wajibi Ne A Hukunta Haramcecciyar Kasar Isra'ila Da Masu Goyon Bayansu

Yau ce Al'ummar kasar Iran suka gudanar da sallar Azumi a fadin kasar baki daya. A nan birnin Tehran, Al'ummar birin sun gudanar da sallar ce bisa Limancin jagoran musulinci Ayyatullah Sayyid Ali Khamnayi.

A hudbar sallar Sayyid Ali khamnayi ya ce abinda ke faruwa a zirin Gaza shine batun farko na Duniyar musulmi a yau, wanda kuma duk wani wanda ke kiran kansa da sunnan dan Adam ya nuna bacin ransa dangane da abinda ke faruwa a zirin Gaza.

Jagoran musulmci ya ce abinda ke faruwa a zirin Gazan kisan kiyashi ne kuma wani bala'I a Tarihin dan Adama, wajibi ne a hukunta masu aikata wannan mumunan Laifi da masu mara masu baya a kotun Duniya

Masu rajin kare hakin bil-adama a Duniya wajine ne su bukaci a hukunta Haramcecciyar kasar Isra'ila

Ayyatullahi Ali Khaimani ya ce duk da cewa Al'ummar Gaza  da kungiyar Gwagwarmaya suna cikin takunkumi, dagewa tare da tsayuwa ga Kalmar gaskiya shi zai basu damar samun Nasara kuma daga karshe nasara na tare da yardar a… 

Jagora ya kara da cewa makiya suna cikin nadama kuma idan suka ci gaba da kai harin ta'addanci to babu shakka yanayin zai kara shiga cikin mawuyacin hali , Amurka da dukkanin Mujuman Duniya suna son dorawa Al'ummar Gaza laifi tare da neman dakatar da buda wuta domin su ceto haramcecciyar kasar Isra'ila 

Yayin da yake ishara kan kokarin makiya da masu girman kai na Duniya wajen ajje makamai gwagwarmaya, Ayyatul khamnayi ya ce duniyar musulmi kamata yayi su taimakawa gwagwarmaya da makamai iya kokarinsu domin tunkarar zalincin haramcecciyar kasar isra'ila. ABNA