5 Yuli 2014 - 07:19
Mutane Ukku Ne Suka Mutu A Masar Ranar Tunawa Da Juyin Mulkin Da Aka Yiwa Mursi

Jami’an tsaro a kasar Masar sun yi amfanin da hayaki mai sa hawaye don tarwatsa maso zanga zanga

Jami’an tsaro a kasar Masar sun yi amfanin da hayaki mai sa hawaye don tarwatsa maso zanga zanga daga cikin

masu goyon bayan tsohon shugaban kasar Mohammad Mursi a jiya a lokacinda suka fito kan titunan wasu birana a kasar don tunawa da cika shekara guda da sojojin suka yi wa tsohon shugaban kasar juyin mulki.

Majiyoyin labarai daga birnin Alkahira sun bayyana cewa jami’an tsaro a garin Al-Jeeza sun kara da masu goyon bayan tsohon shugaban kasar wanda ya kai ga mutuwar mutum guda da jikata wasu da dama.

Hakama a garin Halwan karawa tsakanin magoya bayan mursi ya kai ga mutuwar dansanda guda.

Labaran sun kara da cewa an sami irin wannan taho mu gaman tsakanin jami’an tsaron kasar ta Masar da magoya bayan tsohon shugaban kasar a garuruwan Al-fayyum da Aswan.

Gaba daya dai mutane ukku ne aka kashe a rikin jiyar sannan jami’an tsaro sun kama mutane 20 sun tsare.ABNA