1 Mayu 2014 - 08:50

Asusun bayar da lamuni na duniya IMF ya tallafawa kasar Ukraine da taimakon kudi dalar Amirka Biliyan 17, a yayin da Dakarun Sojin kasar ke tunkarar ‘Yan tawaye masu kishin Rasha. Shugabar Asusun Lamuni Christine Lagarde, tace ya zama wajibi su tallafawa kasar Ukraine saboda makomar tattalin arzikin kasar.

Kudaden na daga cikin rance ne daga Bankin Duniya da kungiyar kasashen Turai suka amince.

Wannan kuma na zuwa a daidai lokacin da Rasha ke barazanar janye Gas din ta take shigarwa zuwa Ukraine.ABNA.