25 Afirilu 2014 - 18:32

Yan Sanda Sun Kame Dan Kasar Lesotho Mai Cin Naman Mutane ‘Yan sandan Afirka ta kudu bisa taimakon ‘yan sanda kasa da kasa (Interpol) sun sami nasarar cafke wani fursuna da ya guba daga gidan yarin kasar Lesotho inda ake tsare da shi saboda kaurin sunar da yayi wajen kashe mutane da kuma cin namansu.

Shi dai wannan mutumin mai suna Makhele Scott dan shekaru 27 a duniya ya tabbatar wa ‘yan sanda da kashe mutane da kuma cin namansu a kasar Lesothon a shekara ta 2012, to sai dai kuma ya gudu daga gidan yarin da ake  tsare da shi don fuskantar shari’a.

Tun a farko-farkon wannan watan ne ‘yan sandan kasashen Afirka ta Kudu da Lesothon bisa taimakon ‘yan sandan kasa da kasa suka gano Mr. Scott a wani coci da ke wajen birnin Durban na kasar Afirka ta kudu inda yayi shigar burtu da ci gaba da rayuwa a cocin.

Bayan kama shi din dai Mr. Scott ya tabbatar musu da aikata wannan laifi na kashe wani dalibi dan shekaru 13 da kuma cin namansa kamar yadda kuma ya tabbatar musu da aikata hakan a kan wani mutum dan shekaru 22 a duniya. Tuni dai aka sake gurfanar da shi a gaban kotu inda kotu da dage sauraren karar zuwa ranar 15 ga watan Mayu mai kamawa da kuma ba da umurnin a ci gaba da tsare shi.ABNA