24 Afirilu 2014 - 20:11
Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan na tattaunawar koli da ta shafi tsaro tare da wasu gwamnonin jihohin kasar, da shugabannin f

Wakilin BBC a fadar Shugaban Nigeria ya ce kawo yanzu gwamnoni 25 sun halarci zaman tare da mataimakan gwamnoni tara.

Manyan hafsoshin tsaron kasar da sufeto janar na yan sanda da kuma manyan jami'an tsaro duk suma suna  cikin tattaunawar.

An gayyaci sarkin Musulmi da Shugaban kungiyar Kiristocin-CAN duk don su bada tasu gudumuwar a taron.

Wannan tattaunawar na zuwa ne a daidai lokacin da Kasar ke fuskantar matsalolin tsaro mussamman ayyukan yan'BOKO Haram.