Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Ƙungiyar makamai ta "Yahya," wadda aka fi sani da "yunkurin Yahya," wadda ta samu sunanta daga sunan shahidi Yahya Sinwar, ta fitar da wata sanarwa inda ta yi barazana ga cibiyar tattalin arzikin Trump da makusantansa a UAE, kuma ta sanar da cewa waɗannan mutane da kamfanoni suna daga cikin manyan wuraren wannan motsi na makamai, kuma za a kai musu hari a kowane yanayi.
A cikin wannan sanarwa yazo cewa manufofin Trump don tabbatar da muradun kansa da na makusantansa sun haifar da ƙaruwar tashin hankali da faɗaɗa rikice-rikicen yankin, kuma wannan kungiya, ta hanyar lura da ayyukan tattalin arziki da sadarwar mutanen da kamfanonin da aka ambata, zata sanya "cibiyar tattalin arzikin Trump a UAE" cikin makasudansa.
Yunkurin Yahya ya buƙaci mutanen da ke da bayanai game da wannan cibiyar su raba bayanai da takardu tare da wannan yunkuri.
Wannan kungiya a baya a cikin sanarwar ta bayyana kanta da cewa: "Muna neman tsarkake duniya daga shaidanu. Muna masu bayyyana maku su. Waɗanda za su iya ɗaukar mataki a duk inda suke a duniya dole su ɗauki mataki. Idan ba ku da ikon ɗaukar mataki amma za ku iya tallafawa, ku tallafa mana ta kowace hanya da za ku iya. Akwai mutane da suka gaji 'yanci da daraja kuma a shirye suke don kowane mataki.
Ku zo mu yi aiki don duk lokacin da zalunci ya kasance a duniya, azzalumai ba za su sami kwanciyar hankali ba, kuma idan dukkanmu muka tashi za mu iya yin wannan aikin. Mun fara! Ku ma za ku iya farawa!"
Kungiyar Yahya a baya ta ayyana wasu daga cikin muhimman wurare da jami'an Isra’ila a cikin jerin makasudanta don ɗaukar fansa ga jinin al'ummar Falasdinu da Gaza da aka zalunta.
……………….
Ra'ayinka